Takardar koyaswa don goyon bayan mata ‘yan kasuwa a sashen noma da sarrafa abinci a Nijeriya

No hay miniatura disponible

Fecha

Título de la revista

ISSN de la revista

Título del volumen

Editor

International Institute of Tropical Agriculture

Resumen

Descripción

Matsawa daga batun samar da kaya zuwa batun neman abin da ake bukata shi ne ya haifar da wannan shiri Na zamantakewar jama’a. Wannan shiri na tattare da manufa na a fara biyan bukatun masu amfana da shirin kafin a gudanar da duk wani abu. Don haka, an gano bukata na horas da mata a fannin noma da kasuwanci a Ibadan da Zaria da ke jihar Oyo da Kadunaa lokacin da aka fara shirin nan na tallafa wa mata ‘yan kasuwa a fannin noma da abinci a Najeriya (SWEAN). Domin a iya horas da mata dangane da gibin da aka gano, shi ya sa aka samar da wannan littafi na horaswa domin Tallafa wa mata ‘yan kasuwa a fannin noma da sarrafa abinci a Najeriya (SWEAN). Takardar na kunshe da ayyuka da dama da aka yi nazarinsu tare da hukumomi masu ruwa da tsaki masu yawa kamar Hukumar Bincike ta Tarayya ta Kamfanoni (Federal Institute of Industrial Research (FIIRO)), Hukumar Binciken kayan Ajiya ta Najeriya (Nigerian Stored Product Research Institute (NSPRI)), Kungiyar Bunkasa Kanana da Matsakantan Kasuwanci ta Najeriya (Small and Medium Enterprise Development Agency of Nigeria (SMEDAN)), Tarayyar Ma’aikata ta Najeriya (Standard Organisation of Nigeria (SON)), Hukumar Ba da Izinin Fitar da Kaya Waje ta Najeriya (Nigerian Export Promotion Council (NEPC)), Kungiyar Raya Sha’anin aikin Gona da Kasuwanci ta Jihar Oyo (Oyo State Agribusiness Development Agency (OYSADA)) da kuma shirye-shiryen Bunkasa sha’anin aikin Noma/ gona (Agricultural Development Programmes (ADP)) a jihar Kaduna. Littafin na kunshe da sassa guda takwas a fannin sarrafa abinci da ingantawa. Sa alama da sawa a leda; ka’idojin da Hukumar NAFDAC take gindayawa domin a yi rajistan abincin da aka sarrafa, ingancin abinci; sayar da rogo da kifi, adanawa da ajiye rahoto; ka’idojin harhada lissafi da harkar kudi a sha’anin kasuwanci da shugabanci da kuma kasuwanci mai nasara. An shirya littafin ne ya zama da amfani ga daidaikun mutane da kuma kungiyoyi wadanda suka ba da kansu wajen horas da mata ‘yan kasuwa a fannin sarrafa abinci a fannin da matan suka fi karkata a kasuwancinsu. Bugu da kari, littafin ya samar da matakai da hanyoyi masu sauki yadda za a iya tabbatar da ingancin abinci domin ci a gida, sayarwa da ma fitar da shi kasashen waje.

Palabras clave

training, nigeria, women, agriculture, food processing

Citación